Shugaban Binance ya tsere daga Najeriya, gwamnatin Tarayya ta bayyana
Bayan shugaban Binance, Nadeem Anjarwalla ya tsere daga Najeriya, gwamnatin Tarayya ta zakulo inda ya ke
Shugaban Binance, Nadeem Anjarwalla, ya tsere daga Najeriya, gwamnatin Tarayya ta zakulo inda ya ke. Gwamnatin ta tabbatar da cewa an samu Anjarwalla ne a kasar Kenya bayan ya tsere daga kulle a Najeriya a kwanakin baya.
Fadar shugaban kasa ta tabbatar da cewa ta haÉ—a kai da sauran hukumomin tsaro da ‘yan sandan Kenya domin dawo da shi Najeriya.
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al’amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja – Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa ta gano inda shugaban Binance da ya tsere, Nadeem Anjarwalla ya ke.
Gwamnatin ta ce ta gano Anjarwalla ya na kasar Kenya bayan tserewar shugaban Binance daga kulle Najeriya a kwanakin baya.
Dalilin haka ne ma ya sa hukumar EFCC da rundunar ‘yan sandan Najeriya da na Kenya suka fara tattaunawa kan yadda za a dawo dashi Najeriya.
Punch ta tattaro cewa Anjarwalla bayan tserewarsa ya gudu ne kasar Kenya domin gujewa hukunci.
Wata majiya daga fadar shugaban kasa ta tabbatar da haka inda ta ce ana ƙoƙarin dawo da shi Najeriya, cewar BusinessDay.
“Mun same shi, mun san inda ya ke, ya na kasar Kenya, muna aiki da wasu hukumomi domin tabbatar da cewa ya dawo Najeriya.” – Cewar majiyar
Hukumomin tsaro a Najeriya da rundunar ‘yan sandan kasa da kasa sun hada kai da ‘yan sandan Kenya domin dawo dashi Najeriya ya fuskanci hukunci.
Hukumar EFCC na zargin Anjarwalla kan wasu laifuffuka biyar da suka shafi rashin biyan haraji da badakalar kudi kimanin $35.4m da sauransu.
Daya daga cikin abokan aikin Anjarwalla, Tigran Gambaryan ya na hannun jami’an EFCC tun a kwanakin baya, cewar rahoton Daily Post.
A baya, mun kawo muku labarin cewa shugaban Binance, Nadeem Anjarwalla ya tsere daga kulle da ake masa a birnin Tarayya Abuja.
Ana zargin Anjarwalla da saba dokokin kasa da suka hada da rashin biyan haraji da sauran laifuffuka.
Daga bisani, mai ba Shugaba Tinubu shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu ya ce sun dauki mataki kan wadanda tsaron Anjarwalla ke hannunsu.